(ḥawsa) حَوْسَ

IBA Montage

Muna gayyatar kamfanin ku don ƙaddamar da aikace-aikacen Kyautar Kasuwancin Kasuwancin Duniya (bugu na 22) a cikin 2025, wanda ke kan gaba a cikin lambobin yabo na kasuwanci na duniya.

Idan kuna son a aiko muku takardun shiga gasar, mai dauke da kaidojin yadda za a shiryawa shiga gasar da kuma mika cikakkun takardun shiga gasar, sai ku shighar da adireshin imel dinku a nan, mu kuma za mu aiko muku su ta imel. Muna da tsarin tsare-sirri mai karfi kuma ba za mu bawa kowa adireshin imel dinku ba saboda kowanne dalili.

 

 

Wannan shafin shi ne kadai za ku gani a wannan shafin na intanet a cikin wannan harshen. Dukkan sauran shafukan suna kunshe ne da bayanai cikin turancin Ingilishi, kamar su ma takardun shiga gasar. Hakan ta faru ne saboda mun bukaci da a gabatar da bukatar shiga gasar cikin turancin Ingilishi, domin kwararru kan harkokin kasuwanci a duk fadin duniya su taka rawa wajen tantance wadanda suka shiga gasar.

 

Game da Gasannin cin Lambar Yabo ta Kasuwanci ta Duniya

Gasannin cin lambar yabo ta duniya su kadai ne gasanni na duniya da suke kimanta nasarori a dukkan bangarori na wuraren aiki. Kungiyar shirya gasannin ta Stevie Awards, wacce take bada lambobin yabon, mazauninta na Amurka. Mu ke shirya gasannin Stevie daban-daban har guda bakwai, wadanda za ku iya samun karin bayani a kansu a www.StevieAwards.com. Gasar cin lambar yabo ta Stevie ta zama daya daga cikin lambobin yabo na duniya da ake girmamawa.

A cikin 2024, an bada lambar yabo ta Lambar Yabo Stevie na Duniya (International Stevie Awards) ga kamfanoni da daidaikun mutane daga kasashe sama da 60. Latsa nan don ganin wadanda suka yi nasara a zangon 2024.

 

Rukuni-Rukuni

Akwai rukuni-rukuni da dama na lambobin yabon da za a iya zaba daga cikin gasar cin lambobin yabo na kasuwanci. Idan kuka zabi shiga gasar, za ku zabi rukunin da ya dace da nasarorinda kungiyar ku ta samu kuma take son a karrama ta a kai, ku kuma shirya takardun shiga gasar bisa kaidojin da aka gindaya. Rukuni-rukunin gasar da ake da su, sun hadar da :

• Lambar Yabo Gwarzon Kamfani na Shekara
• Lambar Yabo ta Hulda da Jama’a
• Lambar Yabo ta yi wa Kwastomomi Hidima
• Lambar Yabo ta Kula da Ma’aikata
• Lambar Yabo ta Hanyoyin Sadarwa na Zamani
• Lambar Yabo ta Gudanarwa
• Lambar Yabo ta Tallata Kasuwanci
• Lambar Yabo ta hanyoyin sadarwa, da suka hadar da shafukan Intanet, Rahotanni na Shekara, Shirya Taruka, da kuma Lambar Yabo ta Bidiyo.
• Lambar yabo ta Kamfanin da ya taka Gagarumar Rawa
• Lambar yabo na Sabon abin da aka Sarrafa

An bayyana jerin sunaye, da bayanan rukuni-rukuni, da abubuwan da ake bukata wajen gabatar da bukatar shiga gasar, da lokacin rufe shiga gasar da ma duk wani kudin shiga gasar, a cikin takardun shiga gasar.

A mafi yawan rukunonin kuna da dama ku aika da bidiyo na minti biyar (5) game da ku ko nasarorin ƙungiyarku a cikin zaɓaɓɓun rukuninku, ko rubutattun amsoshi ga tambayoyin rukunonin.

 

Lambobin Yabo

Za a sanar da wadanda suka lashe Lambar Yabo Stevie na Duniya (International Stevie Awards) 2025 a 13 ga Agusta. Daga baya, za a gabatar da Lambar Yabo na Stevie Award na Azurfa da Tagulla a wani taro a Turai, a watan Oktoba.

 

Tuntuba

A tuntube mu da tambayoyi da ake da su game da gasar Kamfanoni ta Duniya ko kuma kowacce daya daga cikin gasannin cin lambar yabo ta Stevie.

The Stevie Awards
10560 Main Street, Suite 519
Fairfax, Virginia 22030, USA
Lambar Waya: +1 703-547-8389
Fax: +1 703-991-2397
Imel: help@stevieawards.com